An kashe dan gwagwarmaya Ilyas Kashmiri

Ilyas Kashmiri Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ilyas Kashmiri

Wani jagoran 'yan gwagwarmayar Musulunci, Ilyas Kashmiri, ya hallaka a wani harin da Amirka ta kai da jirgin da ba shi da matuki, a yankin arewa maso yammacin Pakistan.

Yana daya daga cikin masu fafutuka 9 da suka rasa rayukansu a daren Juma'a a kudancin Waziristan.

Ilyas Kashmiri shine jagoran Harkatul Jihad al-Islami, wata kungiya mai tsatsauran ra'ayi da ke da alaka da al Qaeda.

Wakilin BBC a birnin Islamabad ya ce, hukumomin Washington za su yi marhabun da mutuwar tasa, saboda da ma shi su ke dora wa alhakin shirya kai hare hare a Pakistan da Afghanistan da kuma India.

Da ma Amirka ta yi tayin bada ladar dala miliyan 5 ga duk wanda ya tsegunta inda Ilyas Kashmiri yake.