An mikawa majalisar dattawan Najeriya sunayen ministoci

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, ya mika wa majalisar dattawan kasar jerin sunayen wadanda ya ke son ya nada a kan mukaman ministoci, domin samun amincewar majalisar.

Kimanin sunayen mutane arba'in ne dai shugaban kasar ya mika, kuma ya bukaci majalisar da ta gaggauta tantance su. Yanzu haka kimanin wata guda kenan da aka rantsar da shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa Alhaji Namadi Sambo, ba tare da majalisar zartarwa ba.