Babban zabe a kasar Portugal

Zabe a Portugal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Portugal

Ana gudanar da babban zabe na kamin cikar lokaci a kasar Portugal, bayan da gwamnatin gurguzu ta nemi kafofin kudade na duniya da su yi belin tattalin arzikin kasar.

Yiwuwar zabtare kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma sharadin da masu belin suka gicciya na kara kudaden haraji, sune suka kankane yakin neman zaben.

Ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa za a fafata sosai tsakanin masu ra'ayin gurguzu da kuma masu matsakaicin ra'ayin yan mazan jiya.

Wakilin BBC ya ce duk wanda ya lashe zaben zai fuskanci babban kalubale wajen aiwatar da sauye sauye marasa farin jini.