An hallaka fiye da mutane 30 a Syria

Zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga zanga a Syria

Masu fafutukar kare hakkin bil'adama a Syria sun ce, dakarun tsaro sun bude wuta akan masu zanga-zanga a birnin Hama na tsakiyar kasar, inda suka hallaka akalla mutane 34.

Rahotanni sun nuna cewa, sojojin gwamnatin sun kuma bude wuta a biranen Homs da Deraa da Deir Ezzour.

Gwamnatin Syrian ta amince cewa, lallai an sami karin zanga zangar, to amma mutane dayawa ba su fito ba.