Shugaba Saleh na kwance a asibitin Yemen

Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh

Mukaddashin ministan yada labaran kasar Yemen ya karyata rahotannin da ke cewar, wai Shugaba Ali Abdallah Saleh ya bar kasar.

Shugaban ya sami raunuka ne a harin da aka kaiwa fadarsa da rokoki, a ranar Juma'a.

Yana can kwance asibiti, fuskarsa da kirjinsa a kone, sannan da wani raunin da ya samu a kasan zuciyarsa, sakamakon fashewar bam.

An ce nan ba da jimawa za a yi masa tiyata

A yanzu haka an kai biyar daga cikin ministocinsa kasar Saudiyya - ciki har da Praministansa - domin yi masu magani, sakamakon munanan raunukan da suka samu a harin.

A daren jiya shugaba Saleh ya watsa sako ta gidan rediyo, inda ya ce yana nan kalau.

Sai dai a yanzu haka ana ta jita-jita a kasar ta Yemen, a kan halin da ya ke ciki.

Harin da aka kaiwa fadar Shugaban ya biyo bayan kwanakin da aka kwashe ana gumurzu, tsakanin dakarun Ali Abdallah Saleh da kuma mayakan kabilu.