Ana gwabza kazamin fada a Yemen

Ana gwabza kazamin fada a Yemen Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yemen na neman fadawa cikin yakin basasa

A kalla mutane 37 ne aka kashe bayan da aka kwashe dare ana gwabza fada a Sanaa babban birnin kasar Yemen, bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe.

Fada ya barke ne bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe tsakanin dakarun gwamnati da magoya bayan Sheikh Sadiq al-Ahmar, shugaban hadaddiyar kungiyar kabilu.

Masu lura da al'amura sun ce fadan na iya jefa kasar cikin yakin basasa.

Yemen na fama da tashe-tashen hankula a sassa da dama na kasar, tun bayan da shugaba Ali Abdullah Saleh ya ki yarda ya sauka daga kan karagar mulki.

Amurka ta nemi shugaba Saleh ya sauka

Wadanda abin ya faru agabansu sun ce ba da labarin kazamin fada, inda kowanne bangare ke zargin dan uwansa da karya yarjejeniyar tsagaita wutar.

A ranar Laraba da safe ma, a bada labarin jin wata kara a Arewacin Sanaa, amma babu dalilin faruwar hakan.

Ma'aikatar tsaron kasar ta zargi dakarun kabilun da kame hedkwatar jam'iyyar General People's Congress mai mulkin kasar a Sanaa.

Ma'aikatan lafiya a birnin sun ce an yi wa duka bangarorin biyu barna.

Mr Saleh, wanda ya shafe shekaru 33 a kan mulki, ya ki sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta sanya shi ya bar mulki.

A ranar Talata, wani mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya nemi shi da ya sauka domin ciyar da kasar gaba.