Tabarbarewar tattalin arzikin Australia

Taswirar Australia
Image caption Tabarbarewar tattalin arzikin Australia

Wasu rahotanni da aka wallafa sun bayyana cewa tattalin arzikin Australia ya yi tabarbarewar da bai taba yi ba a cikin shekaru ashirin da suka gabata.

Rahoton ya ce an samu koma-bayan tattalin arzikin a kasar da fiye da kashi daya cikin dari a watanni ukun farkon bana.

Hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana cewa, ambaliyar ruwan da aka yi a watan Disambar bara, da kuma guguwa mai hade da ruwa da aka yi a birnin Queensland da arewacin kasar, sun yi mummunan tasiri akan tattalin arzikinta.

Hukumar ta kara da cewa, girgizar kasar da aka yi a Japan, ta dagulawa Australia lissafi kasancewar Japan din ce kasa ta biyu mafi girma a cikin kawayen cinikayyar Australiyan.