An sake kai harin bam a jihar Bauchi

Wasu 'yan sandan Niajeriya su na bincike kan harin bam
Image caption Wasu 'yan sandan Niajeriya su na bincike kan harin bam

Rahotanni daga jihar Bauchi a Nijeriya na cewa wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun tayar da bam a wani caji ofis a garin Bulkachuwa inda suka kashe wani jami'in dan sanda guda.

Kakakin rundunar yansandan jihar ta Bauchi ya ASP Muhammd Barau ya tabbatar wa BBC kai harin da mutuwar jami'in dan sandan da kuma kuma ragargaza caji ofis din da maharan suka yi.

Sai dai ya ce maharan ba su yi awon gaba da kome ba daga caji ofis din.

Rundunar yan sandan ta kuma ce tana kan bincike kan al'amarin.

Kawo yanzu dai babu wani mutum ko kungiya da suka dauki alhakin kai harin.