Blatter ya ci zaben shugaban Fifa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Fifa, Sepp Blatter

An zabi Sepp Blatter a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, a karo na hudu.

Blatter mai shekarun haihuwa 75 ne kadai ya tsaya takara duk da cewa dai hukumar FA ta Ingila da kuma Scotland sun nemi da a dakatar da zaben.

Ingila da Scotland dai sun nemi ne da a dakatar da zaben ne saboda zargin cin hancin, daya dabai baiye hukumar, amma dai kuri'u 17 kadai suka samu daga membobin kungiyar.

Blatter ya ci zaben ne da kuri'u 186 daga membobin hukumar 203, kuma zai jagoranci hukumar ne har zuwa shekarar 2015.

"Ina mika godiya, saboda zabe na da kuka yi, kun nuna kwarin gwiwa ne akaina matuka,". In ji Blatter.