An yi mummunan hadarin mota a Katsina

Wani hadarin mota a Najeriya
Image caption Wani hadarin mota a Najeriya

A Najeriya, mutane akalla tara ne suka hallaka a wani mummunan hadarin mota da aka yi a yammacin yau din nan a Katsina.

Hadarin ya afku ne a kan hanyar Katsinar zuwa Kano inda wata motar safa dake makare da mutane ta yi taho-mu-gama da wata karamar mota.

Jami'an hukumar kiyaye hadurran hanyoyi ta kasa da hadin gwiwar jami'an rundunar tsaro ta masu farin kaya ne suka rinka kwasar gawarwakin mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Masu lura da al'ammura dai na ganin cewa rashin kyawon hanya hadi da gudun da ya wuce kiima da wasu direbobi ke yi, su ne babban abinda ke haddasa hadurra da hasarar rayukka a wannan muhimmiyar hanya da ta hada Katsina da Kano.