Zargin aikata laifukan yaki a Libya

Sojojin gwamnatin Libya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojojin gwamnatin Libya

Jami'an Majalissar dinkin duniya masu bincike sun zargi dakarun gwamnatin Libya da aikata laifukan yaki, da kuma cin zarafin bil'adama.

Jami'an hukumar kare hakkin jama'a ta Majalissar sun ce sun gano shaidu na miyagun laifukan da aka aikata da suka hada da kisan kai, da azabtarwa, da hare haren kan mai tsautsayi a kan fararen hula.

Wakiliyar BBC ta ce rahoton ya ci gaba da cewa, bisa la'akari da irin yadda ake wannan keta-haddi, alamu na nuna cewar sai da Mu'ammar Gaddafi , tare da mukarrabansa suka tsara su, kafin a aikata su.

Wakilan Majalissar dinkin duniyar sun ce su ma dakarun 'yan adawar Libya sun aikata laifukka makamantan haka, da za su iya kasancewa na yaki, kodayake yawansu bai kama kafar na dakarun gwamnati ba.