Gobara a cibiyar rigakafi ta kasa a Borno

Image caption Cibiyar Rigafi na kasa a Borno bayan ta kone kurmus

Dukiyoyi na miliyoyin Nairori ne suka kone kurmus sakamakon gobarar da ta tashi a Cibiyar Lura da Annoba da Allurar Rigakafi ta Kasa NPI a jihar Borno.

Gobarar dai ta kona na'urorin sanyaya alluran rigakafi, magunguna,motoci da kuma tan tan na kayan abinci.

Gobarar ta shafi wasu manyan dakunan ajiyar kayan abinci da gidajen jama'a dake kusa da cibiyar.

A yayin da dai mazauna Unguwar Doki inda lamarin ya faru suka bayyana jin karan bindigogi da kuma wata fashewa kafin tashin gobarar.

Hukumomin gwamnatin sun tabbatar da abkuwar lamarin ne da cewar gobarar ta tashi ne bayan da wasu mutane suka shiga cibiyar da wasu abubuwa da ake kyautata zaton man fetur ne suka kuma bankawa wurin wuta.