Yunkurin satar bayanan shafukan intanet

Tambarin kamfanin Google
Image caption Google ya ce an yi yunkurin sace bayanan intanet

Kamfanin shafin intanet na matambayi baya-bata, wato Google ya ce masu satar bayanan intanet sun yi yunkurin sace bayanan email din mutane da dama.

Kamfanin ya ce masu satar bayanan, sun aikewa mutane da dama sakonnin email na jabu da zummar ganin sun kwace akalar gudanar da shafukan mutanen.

Ya kara da cewa mutanen da aka aikewa da sakon email na jabu sun hada da jami'an gwamnatin Amurka, da 'yan siyasar China, da sojoji, da 'yan jarida da kuma jami'an gwamnatocin nahiyar Asia.

Ya ce masu satar bayanan sun fito ne daga kasar China.

Fadar White House dai ta ce, tana gudanar da bincike kan wannan batu, sai dai ta kara da cewa, babu wani bayani na email din ma'aikatanta da ya bata.