Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Kyakkyawar kulawa ga mace mai jego

Image caption Matan da ke jego na bukatar kulawa ta musamman

Kyakkyawar kulawa ga mace mai jego da kuma jaririnta musamman ma a kwanaki da makwannin farko bayan haihuwa abu ne mai mahimmancin gaske.

A cewar shafin intanat na wikipedia mace mai ciki na fara jego ne da zarar ta haihu.

Kuma a wannan lokacin ne jikinta ke kokarin komawa yadda yake a da gabannin samun ciki.

Inda shafin ya kara da cewa abu mafi mahimmanci a lokacin da mace ta samu kanta cikin jego shi ne kasancewarta cikin koshin lafiya ta yadda za ta iya kula da sabon jaririnta.

Shafin na wikipedia ya kuma bayyana cewa akalla kashi 25 cikin dari zuwa kashi 85 cikin dari na samun kansu cikin rashin jin dadi na wasu 'yan kwanaki.

Yayin da kashi 7 cikin dari zuwa kashi 17 cikin dari na matan dake jego kan fada cikin halin matsanancin damuwa.

To wadannan al'adu dake kama da al'adar Bahaushe na nuni da cewa ba malam Bahaushe ne kadai ya san muhimmancin hutu da kyakkyawar kulawa ga mace mai jego ba.

Kodayake ko a cikin Hausawanma ba duka aka taru aka zama daya ba, domin wasu magidantan kan gudu su bar ladansu na kula da mai dakinsu data haihu da sabon jariri ko jaririya.