'Yaki da shan miyagun kwayoyi bai yi nasara ba'

Wani mutum da ke ta'ammali da miyagun  kwayoyi
Image caption Yaki da miyagun kwayoyi ya gaza

Wata kungiya da ta kunshi shugabannin kasashen duniya, da masu fada-aji, ta yi kakkausar suka kan salon da ake amfani da shi, wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.

A cikin wani rahoto da kungiyar maisuna The Global Commission on Drug Policy ta fitar, ta ce akwai bukatar gudanar da sauye-sauye kan dabarun yaki da shan miyagun kwayoyi.

Ta kara da cewa, shirin yaki da miyagun kwayoyi a duniya ya yi sanadiyar karuwar laifuka ne, kana ya sanya aka kashe miliyoyin kudade, da sanadiyar rasa rayukan mutane da dama.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar auna mizani shan kwayoyi

Rahoton ya yi kira da a kawo karshen musgunawar da ake yiwa mutanen da ke ta'ammali da miyagun kwayoyi, wadanda kuma basa kai hari ga jama'a.

Manyan mutanen da ke da hannu wajen fitar da rahoton sun hada da tsoho shugaban majalisar dinkin duniya, Kofi Annan, da dan kasuwar nan Sir Richard Branson.