Garabasar motoci ga 'yan majalisar Najeriya

Motocin 'yan majalisa
Image caption 'Yan majalisar sun ce ba arha ba ce

A Najeriya, a yau ne majalisun dokokin kasar suka yi zamansu na karshe a wannan jumhuriya ta shida.

Mafi yawan zaman dai sun cinye shi ne wajen jawaban bankwana da juna, musamman ma ga takwarorinsu da ba su samu komawa majalisun ba.

Sai dai majalisar wakilan kasar ta yi wata garabasa wa mambobinta, inda ta sayar musu da motocin da suka yi aiki da su a zamansu na majalisar a kan farashi mai rahusa, lamarin da wasu ke gani kamar an karya darajar motocin fiye da kima.

Amma `yan majalisar sun musanta ce sun sami garabasa. Suna ganin sun saya a daidai farashin kasuwa.