Fiye da mutane ashirin sun mutu a Pakistan

Sojojin Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun soji sun mutu a Pakistan

Jami'ai a Pakistan sun ce akalla dakarun sojin kasar ashirin da uku ne suka rasu a wata gwabzawa da suka yi da dakarun sa-kai a kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan.

Fafatawar ta faro ne tun a jiya Laraba inda mayakan sa-kai kimanin dari biyu suka tsallako daga Afghanistan domin kai hari a kafofin bincike na jami'an tsaro.

Jami'an Pakistan dai sun ce kawo yanzu babu cikakken bayani akan fafatawar, saboda hanyar sadarwa a yankin ta katse.

Ba a tabbatar da ko wacce kungiyar mayakan sa kai ce ta kai harin ba.