Rasha ta haramta kayan lambu daga Turai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kayan lambu ya kashe akalla mutane 16 a Turai sanadiyar cutar Ecoli.

Tarayyar turai ta bayyar da sanarwar cewa Rasha ta yi azarbabi da ta harmata shigar da kayan lambu kasarta daga kasashen Tarayyar Turai.

Babban jami'in lura da harkokin lafiya Gennady Onishchenko ne ya bayar da wannan sanarwa, inda yace barkewar annobar Ecoli a kasar Jamus ta zarce yadda ake zato.

Rasha dai ta yi wannan barazana a farko wannan mako, saidai duk da haka matakin ya baiwa manoman kayan lambun turai mamaki.

Kasuwannin Rasha sun ci gaba da gudana, duk da rudanin da aka samu, sakamakon barkewar cutar E-Coli a kasar Jamus, wadda a halin yanzu ta karade kusan daukacin nahiyar turai.

Babban jami'in kula da lafiya na kasar Rasha, kuma shugaban hukumar kare masu amfani da kayayyaki a kasar, Gennady Onishchenko ya ce ya bullo da wannan haramci ne saboda an kasa shawo kan lamarin a cikin tsawon wata guda.

"Mace macen da aka samu a kasar Jamus ya nuna karara cewa, irin dokokin kare muhalli da ake amfani da su a Turai wanda ake ta yayata cewa ya kamata Russia ta yi aiki da su, ba su da wani amfani." In ji Gennady Onishchenko

Wani kakakin hukumar tarayyar turai ya ce tarayyar turai za ta aikawa Rasha wasika nan gaba kadan, inda za ta bayyana haramcin da Rasha ta yi da cewa bai dace ba.

Kashi 3 cikin hudu na kayan lambun da turai ke fitarwa ketare na zuwa ne kasar Rasha. Kasashenda suka fi fitar da kayan lambun su ne Netherlands da Poland.

Wasu manoman turai sun yi zargin cewa, haramcin wata manufa ce ta taimakawa manoman Rasha su samu kasuwa a daidai wannan kaka ta shekara.