An raunata shugaba Saleh na Yemen

Yemen
Image caption Kungiyoyin kabilu masu dauke da makami na ci gaba da jan daga

Jami'ai sun ce wani harin roka da aka kai fadar shugaba Abdallah Saleh na kasar Yemen, ya yi sanadiyyar raunata shugaban tare da wasu mukarrabansa.

An kuma raunata Fira Ministan kasar da kuma kakakin Majalisar Dokoki, sannan aka kashe wasu masu gadin shugaban uku.

Mataimakin ministan sadarwa na kasar Abdu al-Janadi ya shaida wa manema labarai cewa: "Mai girma shugaban kasa na cikin koshin lafiya, kuma ya fasa gudanar da taron manema labaran da ya shirya gudanarwa......saboda kurjewar da ya yi. In Allah ya yarda zai warke." Ya kara da cewa babu abin da ya samu lafiyarsa, kuma tuni aka kaddamar da bincike kan harin.

Tunda farko dakarun gwamnati sun kai hari kan gidan dan uwan shugaban kungiyar kabilun da ke fada da dakarun gwamnati.

Sai dai ofishin shugaban kungiyar kabilun, Sheikh Sadeq al-Ahmar, ya nesanta kansa da harin da aka kai fadar shugaban.

Wannan ya sabawa bayanan farko da suka fito daga mai magana da shi, wanda ya ce harin na ramuwar gayya ne.

A bangare guda kuma, dubban mutane ne suka halarci jana'izar mutane 50 da aka kashe a rikicin.