'Yan adawa sun yi kiran saukar shugaban Syria

Shugaba Assad Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana ci gaba da kashe masu zanga-zanga a kasar

Kungiyoyin adawa na Syria wadanda ke taro a Turkiyya sun yi kira ga Shugaba Assad ya ajiye aiki nan take, ya kuma ba da dama kasar ta koma kan turbar dimokuradiyya.

Masu fafutuka kusan dari uku ne, wadanda akasarinsu ke gudun hijira, ke halartar taron.

Kungiyoyin sun yi watsi da tayin Shugaba Assad na hawa teburin shawara da kuma afuwa ga masu zanga-zanga, sannan suka sha alwashin yin abin duk da za su iya don kawar da shi daga kan mulki.

A can kasar ta syria kuwa, jami'an tsaro sun ci gaba da yunkurinsu na murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati ta hanyar yin luguden wuta da bindigogin atilari da tankokin yaki a garin Rastan.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary clinton, ta ce halascin mulkin Shugaba Assad na gab da karewa.

Ta ce idan ba zai iya kawo karshen muzgunawa al'ummarsa ba, kuma ba zai iya daukar matakai na hakika don kawo sauyi ba, to ya kamata ya koma gefe ya ba wasu dama.