Ana ci gaba da fafatawa a Sana'a

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun gwamnati da mayakan kabilu na ci gaba da budewa juna wuta

Fada ya kazanta a babban birnin Yemen, Sana'a bayan da dakarun dake biyayya ga Shugaba Saleh da kuma mayakan kabilu suke ci gaba da budewa juna wuta.

Rahotanni sun ce dubban mayakan kabilu ne suke so su kutsa cikin bangaren dake karkashin ikon gwamnati a arewacin Sana'a.

Ana dai ganin wasu sun samu shiga wadanan yankuna, saboda wandanda suka gane wa idonsu sun ce mayakan na dauke da manyan makamai.

A yanzu haka dai babu jirgin dake sauka a filin saukar jiragen sama na Sana'a, saboda yakin da ake yi a kasar, amma wani darekta a filin jirgin saman ya ce abubuwa zasu daidaita.

Daruruwa mutane ne suka rasa rayukansu kuma da dama suka jikkata bayan da aka fara yaki kwanaki biyu da suka wuce.