A yau Ratko Mladic zai bayyana a gaban kotu

Image caption Ratko Mladic

A yau ne tsohon komandan sabiyawan Bosniya Ratko Mladic zai bayyana a karon farko a kotun laifukan yaki dake Hague

Ana zarginsa da aikata kisan kiyashi da kuma laifuka akan bil adama dake da alaka da yaki a Bosnia a shekarun 1990.

Baban me shigar da kara ya ce Mr Mladic ya gudanar da munana laifukan da suka raba kasa.

Yanzu dai shekarun Mr Mladic sistin da tara kuma lauyansa Alexander Alexic ya ce zai shigar da koke kan rashin koshin lafiyar mutumin da yake karewa.

kotun zata tambaye Mr Mladic akan ko ya fahimci zargin da ake masa da kuma ko yana son ya shigar da koke, idan har be mayar da martani nan da kwanaki talatin masu zuwa ba alkalan kotun zasu shigar da koken rashin amincewa da aikata laifi a madadinsa.