An sake yiwa kamfanin Sony sata.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kamfanin playstation na Sony

Wata kungiyar masu satar bayanan komputa dake kiran kanta Lulsec tayi ikirarin sace adreshin e -mail fiye da miliyan daya da kuma wasu bayanai daga masu amfani da wani shafi mai farin jini da katafaren kamfanin lataroni na Sony ke gudanarwa.

Wannan gagarumar satar bayanai da aka yiwa shafin kamfanin na Sony Pictures dot com,shine na baya bayanan a 'yan makonnin nan.

A baya dai an sace wasu bayanan Playstation wani reshe na kamfanin Sony.

Hakan dai, ya sa an rufe kamfanin Playstation din kusa da wata daya.

Tuni dai kamfanin sony ya ce ya fara gudanar da bincike kan wanan batu.