Ranar jimamin yaran da aka hallaka a Syria

Rahotanni daga kasar Syria na cewa, an samu karuwar zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a duk fadin kasar bayan sallar juma'a.

Masu fafutuka a kasar sun ware yau ta zama ranar jimamin yara kanana fiye da talatin da suka ce, an hallaka tun da aka fara tarzoma a kasar cikin watan Maris.

Masu fafutuka a kasar ta Syria sun kuma ce, mutane dubu dari ne suka yi zanga-zanga a birnin Hama dake tsakiyar kasar, kuma jama'a sosai sun fito a sauran sassan kasar.

Wakilin BBC yace za'a kai sa'o'i nan gaba kafin a gano irin zubar da jinin da boren na wannan makon ya haddasa, kuma kasashen duniya sun sa ido suna kallon abinda ke faruwa a kasar cikin damuwa.