Yunkurin kama kakakin Majalisar wakilan Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Wasu rahotanni sun ce kakakin Majalisar wakilan Najeriya me barin gado Hon Dimeji Bankole ya aikawa Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati wato EFCC wasika, yana cewa da zarar ya mika ragamar shugabancin majalisar a ranar litinin zai kai kansa a ofishin hukumar.

Daga bisani, hukumar EFCCn, ta yi yunkurin kame Hon. Bankole, al'amarin da ya kai ga sa-in-sa tsakanin jami'an hukumar da kuma jami'an dake tsaron lafiyar Kakakin Majalisar.

Hukumar ta EFCC dai ta gayyaci Hon. Bankole ne ya bayyana a gabanta, domin ya wanke kansa daga zarge-zargen da ake masa na karkatar da wasu kudaden Majalisar.

Na hannun damansa dai sun ce kakakin Majalisar bai amsa gayyatar bane saboda hukumar ta EFCC bata bi hanyoyin da suka dace ba, wajen mika bukatar ta.