Mai yiwuwa an gano tushen cutar E-coli a Jamus

Tsiron wake Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsiron wake

Jami'ai a Jamus sun ce a yanzu sun yi amunnar wani nau'in wake ne da ake nomawa a kasar mai yiwuwa musabbabin cutar nan ta E.Coli mai haddasa tsananin zawo da amai da ma zazzabi.

Kawo yanzu mutane 22 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar, sannan wasu dubu 2 sun kamu a cikin Jamus din da kuma waje.

Ministan aikin gona a yankin Lower Saxony, Gert Lindermann ya ce, masu binciken annoba sun danganta tushen annobar da wata gona a Uelzen, kimanin kilomita 400 a kudancin Hamburg.

Ministan ya ce an rufe gonar, kuma an janye dukan amfanin gonar daga kasuwanni - duk da cewa har yanzu gwajin hukuma bai tabbatar da kasancewar kwayoyin cutar a gonar ba.