'Isra'ila ta kashe masu zanga zanga a Tuddan Golan'

Zanga zanga a Tuddan Golan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga zanga a Tuddan Golan

Gidan talabijin din Syria ya ce, mutane 20 sun hallaka, kuma wasu fiye da 300 sun jikkata, lokacin da dakarun Isra'ila suka bude wuta a kan magoya bayan Falasdinawa masu zanga zanga.

Mutanen suna kokarin shiga yankin tuddan Golan da Isra'ilan ta maye ne, ta bangaren Syria.

Masu zanga zangar suna tunawa ne da ranar da yakin kwana shidda na 1967 ya barke. A lokacin ne Isra'ila ta kwace Tuddan Golan.

Kawo yanzu Isra'ila bata ce komai ba game da mutanen da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata.

Gwamnatin Isra'ilan ta ce, hukumomin Syria ne suka shirya zanga zangar, domin kawar da hankula daga matakin da su ke dauka na murkushe masu adawa da su a kasarsu.