Kungiyar NATO ta sake kaiwa Libya hari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani wuri da aka kaiwa hari a Libya

A cikin dare ne dai jiragen sama masu saukar angulu na kungiyar tsaro ta NATO su biyu suka tashi daga jirgin ruwan soji na Birtaniya,inda suka kai hari a naurar hange nesa ta soji da kuma wurin gudanar da bincike na soji a garin Brega.

Hakazalika a dai dai wanan lokacin jiragen sama masu saukar angulu na kasar Faransa su ma suka kai hari a wuraren da suka hada da motocci soji, da kayayakinsu da kuma dakarun dake kasa.

Kungiyar ta NATO ta ce komai ya tafi dai dai a hare haren da suka kai kuma tuni har jiragen saman masu saukar angulu suka dawo. Wanan dai shine karon farko da kungiyar NATO zata yi amfani da jiragen sama masu saukar angulu akan dakarun kanar Gaddafi.

Ta ce amfani da jiragen sama masu saukar angulu ya kara bata damar neman da kuma kaiwa dakarun dake biyaya ga kanar Gaddafi farmaki domin hanasu kaiwa farar hula hari.