An kara kashe masu zanga zanga a Syria

Zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga zanga a Syria

Masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Syria sun ce, dakarun tsaro sun harbe mutane ukku har lahira a garin Jisr Al-Shugour na arewacin kasar.

Garin dai ya kasance wurin zanga zanga tun lokacin da aka soma tada wa Shugaba Bashar Assad kayar baya, a cikin watan Maris.

Tun farko dai dubun dubatar mutane sun fita a birnin Hama, domin jana'izar masu zanga zangar da dakarun tsaro suka kashe a jiya Juma'a.

Masu fafutukar na Syria sun ce, mutane akalla 60 ne suka mutu a lamarin da ya mafi muni tun barkewar tarzomar.