Amurka ta yi Allah wadai da rikicin Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin kasar Yemen

Gidan talabijin na kasar Yemen ya watsa wani takaitaccen sako daga shugaba Ali Abdullah Saleh, fiye da sa'oi shida bayan daya samu rauni a wani hari na roka da aka kai a harabar gidansa dake babban birnin kasar na Sana'a.

Amma gidan talabijin din bai nuna hoton Shugaba Saleh ba, sai dai muryarsa ce kawai aka ji, inda yake dora alhakin harin da aka kai a cikin gidan nasa akan gungun da basa ga miciji da kabilarsa.

Shugaban ya ce zasu zakulo masu laifi nan bada jimawa ba, tare da hadin kan dakarun tsaro.

Ya kuma ce mutane bakwai aka kashe a harin, wadanda suka hada da mataimakin firaministan kasar Rashad Al-Alimi.

Tuni dai Amurka ta yi Allah wadai da tashin hankalin Yemen, kuma tayi kira ga dukannin bangarorin akan su yi hakuri kuma su yi abun da ta kira gudanar da shirin mika mulki cikin kwanciyar hankali.