Ana cigaba da takaddama akan kakakin Majalisar wakilai na Najeriya

A Najeriya, yayin da ake shirin kaddamar da Majalisar wakilai ta kasa a Jamhuriya ta bakwai gobe, wasu zababbun 'yan Majalisar daga jam'iyyar PDP sun ce bakin alkalami ya riga ya bushe, a yunkurinsu na zaben Kakakin majalisar wanda ba jam'iyyar ce ta fito da shi ba.

Sabani ya kunno kai ne dai tsakanin uwar jam'iyyar ta PDP da wasu daga cikin zababbun 'yan majalisar ta wakilai, bayan jam'iyyar tace ta ware mukamin kakakin majalisar ga shiyyar kudu maso yammacin kasar.

Tuni dai shugaban jam'iyyar na kasa, Dokta Bello Halliru dama Shugaban kasar Goodluck Jonathan, suka yi kira ga 'yan Majalisar dasu yi biyayya ga umurnin jam'iyyar, suna masu cewa ba za'a lamuncewa rashin da'a ba.

Hon. Ibrahim Bawa Kamba, zababben dan majalisar ne daga Jihar Kebbi, kuma ya shaidawa BBC cewa su masu biyayya ne ga jam'iyya, amma ba zasu sauya matsayi ba.

Ya kuma ce idan har aka basu mutumin da basa so, zasu tsige shi ba tare da bata lokaci ba.