Zaben Tambuwal ya bude sabon babi a Najeriya

majalisa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harabar majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ci gaba da tsokaci dangane da zaben Alhaji Aminu Waziri Tambuwal daga shiyyar Arewa maso yammacin kasar a matsayin kakakin majalisar.

Zaben dai ya ja hankalun jama'a da 'yan siyasa da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum saboda ya sabawa umurnin uwar jam'iyar PDP wacce ta ce a zabi Mulikat Adeola Akande daga shiyyar Kudu maso yammacin kasar bisa ta farkin jam'iyyar na karba karba.

Dr Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya shaidawa BBC cewar zaben kakakin majalisar wakilai din ya bude wani sabon babi a tsarin mulkin demukradiyyar Najeriya.

Anasu bangaren, 'yan majalisun dokokin kasar sun ci gaba da bayyana aniyarsu ta inganta rayuwar al`umma bayan sun yi rantsuwar kama aiki. Mafi yawa dai na ikirarin dukufa wajen ganin gwamnati ta wadata al`umomin da suke wakilta da abubuwan more rayuwa.

To sai dai an dade ana zargin `yan majalisun, da daukar irin wadannan alkawura amma daga baya sai hankalinsu ya koma kan wasu bukatun da ke gabansu.