Shugaba Jonathan ya sa hannu kan dokar yaki da ta'addanci

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sanya hannu akan dokar yaki da ta'addanci da kuma dokar yaki da halasta kudin haram.

Ita dai dokar ta yaki da ta'addanci za ta taimaka ne wajen aiwatar da kudurin majalisar dinkin duniya akan yaki da ta'addanci.

A baya-bayan nan dai Najeriya tana fuskantar kalubalen tsaro ta fuskoki da dama.