Mutane biyu sun hallaka a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Gaddafi

Jami'an Libya sun ce kungiyar tsaro ta NATO ta kaiwa wata anguwa a birnin Tripoli hari ta jiragen sama.

An dai lalata wani gini mai hawa biyu a anguwar Sug El Juma, kuma an fitar da gawarwakin mutane akalla guda biyu.

Ma'aikatan ceto na kokarin ceto rayukan mutane dake karkashin baraguzan ginin da suka ruguje.

Hakazalika daruruwan mutane sun taru a wurin domin neman sauran gawarwakin mutane,wasu na fadin cewa akwai iyalin da suka hallaka gabakidayansu.

Sai dai harin baya bayanan zai kara janyo tambayoyi akan abun da kungiyar tsaro ta NATO ke yi da kuma nasararorin da take samu a kasar ta Libya, musaman a kasashe da suka nuna shaku akan shirin kaiwa kasar farmaki .