Zanga zangar rashin amincewa da sabon kundin tsarin mulkin Morocco

A yau za'a gudanar da zanga zanga a wasu manyan biranen kasar Morocco da dama, bayan wata kungiyar masu fafutukar neman sauyi taki amincewa da wasu canje canje a cikin kundin tsarin mulkin kasar da Sarki Mohammed yake neman ya aiwatar.

Kungiyar dai na cewar wadannan sauye sauye ba suyi ba.

Masu suka da dama dai na bukatar ganin cewar dukkanin sauyen sauyen da za'a aiwatar, ya zamana cewar wani kwamitin mutanen da aka zaba ne zasu yi su.

Sun kuma ce zaben raba gardamar da ake shirin yi akan kundin tsarin mulkin kasar ya yi sauri, kuma bai bada isashen lokacin da za'a tafka mahawara akai ba.

A ranar juma'a ne dai Sarki Mohammed yace sauyen sauyen da za'a yiwa kundin tsarin mulkin, zai takaita karfin da yake dashi, kuma zasu sanya kasar Moroccon kan hanyar tsarin mulki irin na masarauta.