A yau za'a ranstar da sabbabin yan Majalisun dokokin Najeriya

A Najeriya, a yau ne ake sa-ran majalisun dokokin kasar zasu fara aiki a karkashin sabuwar Jamhuriya ta bakwai.

Kuma a yau dinne mambobin majalisun zasu sha rantsuwar kama aiki, tare da zabar shugabannin da zasu jagorance su.

Rahotanni dai na nuna cewa akwai yiwuwar zaben ya gudana cikin ruwan-sanyi a bangaren majalisar dattawan kasar, saboda wani gyaran-fuska da majalisar tayi wa dokokinta.

Amma a bangaren majalisar wakilai, mai yiwuwa a kaiga tada-jijiyar-wuya, sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu a majalisar dangane da zaben shugabannin.

Tuni dai wasu 'yan majalisar wakilan kasar suka fara zargin bangaren zartarwa, da yin barazanar yunkurin amfani da karfin mulki wajen tilasta musu akan su zabi sabon kakakin Majalisar.

A cewar wasu daga cikin 'yan Majalisar wakilan, akwai yunkurin amfani da kudade don ganin an sauya ra'ayin 'yan majalisun wajen zaben kakakin Majalisar.

Sai bangaren zartarwar kasar ta musanta wanan zargi.