Bai kamata a danganta fashe-fashen bama-bamai da addini ko siyasa ba, in ji Mark

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, David Mark yace, bai kamata a rika danganta tashe-tashen bama-baman dake faruwa a Najeriya da addini ko siyasa ba.

Ya kuma ce, lamarin kalubalen ne mai tada hankali da ya kamata ace hukumomin tsaron kasar su shawo kai.

A hirar da yayi da BBC, shugaban majalisar dattawan ya ce, kamata yayi hukumomin tsaro suyi aiki tare, kana su gujewa yin gasa tsakaninsu.

A cewarsa kamata ya yi a koyi da darasi daga wanan lamari daya auku, domin kuwa wasu sun samu bayanai tsaro amma basu yi amfani da shi yadda ya kamata ba.

Senata Mark ya yi kira ga hukumomin tsaron kasar akan su sake lale dangane da yadda suke gudanar da aiyukansu musaman wuri musayar bayanai.

Harin bama-baman da aka kai a ranar Alhamis a hedikwatar 'yan sandan Najeriya dai, yayi sanadiyyar mutuwar mutane shida, da kuma raunana wasu da dama.