Tambuwal ne sabon kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Sabon kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal

Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne ya lashe zaben kakakin Majalisar dokokin Najeriya bayan da ya doke abokiyar takararsa Mrs Mulikat Akande Adeola.

Nasarar da Alhaji Tambuwal ya samu a Majalisar ya rushe tsarin karba-karba da Jam'iyyar PDP ta shirya na mika kujerar ga shiyar kudu maso masu yammacin kasar a majalisar.

Alhaji Aminu Tambuwal dai ya lashe mukamin shugaban majalisar ne da babban rinjaye inda ya samu kuri'u 252 bisa na Mulikat da ta samu 90.

Tuni dai akawun Majalisar ya rantsar da shi a matsayin kakakin Majalisar Wakilai.