Hukumar lura da yanayi ta yi hasashen ruwan sama sosai a Nijer

Hakkin mallakar hoto bbc

A jamhuriyar Niger hukumar kula da yanayi ta kasa ce ta yi wa 'yan kasar wani albishir na cewa, hasashen da ta yi cewa bana za a sami ruwan sama mai yawan gaske a duk fadin kasar.

Abun da ke nuna cewa za'a samu damana mai kyau a bana a kasar ta Niger in Allah ya yarda.

Sai dai hukumar kula da yanayin ta kasa ta yi gargadin cewa akwai alamun samun ambaliyar ruwa a kasar a bana ma.

Kasar Niger dai ta sha fuskantar matsalolin karancin abinci a 'yan shekarun baya-baya nan, sakamakon karancin ruwan sama, har ma da ambaliyar ruwa a wasu yankunan kasar a bara.