An rantsar da majalisar dokoki a Nijeriya

Hon Aminu Waziri Tambuwal Hakkin mallakar hoto google
Image caption Hon Aminu Waziri Tambuwal

A Najeriya, a yau ne aka kafa sabuwar jamhuriya ta bakwai inda majalisun dokokin kasar suka gudanar da zaben shugabanni tare da shan rantsuwar kama aiki.

Tsohon shugaban majalisar dattawan kasar, Senata David Mark ne ya sake zama shugaban majalisar ba tare da wata hamayya ba, yayin da su kuma`yan majalisar wakilai suka zabi Hon Aminu Waziri Tambuwal a matsayin sabon kakakin majalisar.

Hon Tambuwal dai ya yi takara ne da Mrs Mulikat Akande-Adeola, wadda ta fito daga shiyyar kudu maso yamamcin Nigeria, yankin da tun farko jam'iyyar PDP ta ware wa wannan mukami, amma 'yan majalisar suka zabi Alhaji Aminu Tambuwal din, wanda ya fito daga yankin arewa maso yammacin kasar.