Bama bamai sun tashi a Maiduguri

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun nuna cewar, kimanin mutane 5 ne suka rasu, kuma dayawa sun sami munanan raunuka, sakamakon tashin bama bamai yau da rana a Maiduguri.

Bam din farko ya tashi ne tsakanin Caji ofis na Metro da kuma Cocin Saint Peters, inda nan take ya raunata mutane uku yayin da mutum guda ya rasu.

Bam na biyu ya fashe ne kusa da Caji Ofis na Dandal dake tsakiyar birnin.

Sai kuma na ukun wanda ya tashi a tsakanin makabarta da Caji Ofis na unguwar Gwange.

Rundunar 'yan sandan jihar Bornon ta tabbatar da abkuwar wannan lamari, tare da dora alhakin hare haren kan kungiyar Boko Haram.