An sami fashe-fashe a Maiduguri

Kwamishinan 'yan sanda Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwamishinan 'yan sanda

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno, na cewar wasu abubuwa guda biyu sun fashe a cikin birnin, inda kawo yanzu aka ce an kai gawawwakin mutane biyar zuwa asibitin koyarwa da ke birnin.

Haka nan kuma rahotannin sunce a yanzu haka ana can ana jin karar harbe-harbe a Unguwar Gwange da ke cikin birnin. Kawo yanzu babu cikakken bayani akan wannan al'amari.

Birnin na Maiduguri dai na fama da tashe-tashen hankulla sanadiyar aikace aikacen 'yan kungiyar da aka fi sani da kungiyar Boko Haram.