Shugabannin Sudan na tattaunawa a Habasha

Sojan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Abyei Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Abyei

Shugaban kasar Sudan da takwaransa na Kudancin Sudan na wata ganawa da nufin kawo karshen takaddamar da ta barke a kan iyakar kasashensu kasa da wata guda kafin samun 'yancin Kudancin.

Ma'aikatan agaji sun ce kusan mutane dubu dari da arba'in ne dai suka tsere daga gidajensu don gujewa rikicin.

Kungiyar Tarayyar Afirka ce dai ke karbar bakuncin tattaunawar tsakanin Shugaba Omar al-Bashir da kuma Salva Kiir na Kudanci.

Ballewar kudancin dai ya biyo bayan rikicin da suka kwashe shekara da shekaru suna tafkawa ne da arewaci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan miliyan daya da rabi.

Fadan da aka fafata a kan iyakar kasashen ya kawo fargabar za a sake komawa bakin daga.

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu da Firayim Minista Meles Zenawi na Habasha ne ke shiga tsakani a tattaunawar, wadda ta ke gudana a babban birnin kasar ta Habasha, wato Addis Ababa.

Wata sanarwa da Kungiyar Tarayyar turai ta fitar ta nuna cewa tattaunawar za ta mayar da hanakali ne a kan janye sojoji daga garin Abyei, wanda ake takaddama a kansa, wand kuma sojoji arewaci suka mamaye a watan da ya gabata.

A cewar sanarwar, tattaunawar za ta duba "yadda za a girke wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasa-da-kasa wadda nahiyar Afirka ke jagoranta, don ta samar da tsaro da kuma kyakkyawan yanayi don a mayar da wadanda rikicin ya raba da gidajensu cikin gaggawa, a kuma kawo karshen ce-ce-ku-ce a kan matsayin yankin".

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani jami'in diflomasiyya da bai ambaci sunansa ba yana cewa Shugaba Bashir ya amince ya janye dakarunsa daga garin sai dai har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, wadda ake sa ran za ta hallara a birnin na Addis Ababa a yau Litinin, za ta gana da Mista Kiir amma ba za ta gana da Mista Bashir ba, kamar yadda daya daga cikin masu yi mata hidima ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi gargadin cewa magoya bayan sojojin arewaci na tursasawa magoya bayan kudanci a jihar Kudancin Kordofan wadda ke arewaci amma kuma take da al'ummun kudanci masu yawa.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Sudan, Suna, ya ambaci wani jami'in arewaci yana gargadin gwamnatin kudanci ta guji marawa 'yan tawaye baya a Kudancin Kordofan.

Sai dai wani jami'in soji a kudanci ya musanta cewa akwai dangantaka tsakanin sojojin kudanci da kungiyoyin da ke goyon bayan kudanci wadanda ke tayar da kayar baya a Kudancin Kordofan duk kuwa da cewa su ma bangare ne na 'yan tawayen da suka yi shekaru suna yaki da arewacin.