Jakadiyar Syria a Faransa ta yi murabus?

Mata da yara na ficewa daga Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mata da yara na ficewa daga Syria

Rahotanni na sabawa juna dangane da makomar jakadar Syria a Faransa, Lamia Chakkour.

Gidan talabijin din Faransa ya bada wata sanarwar da ya ce daga gareta ne, inda ta ke cewa ta yi murabus daga aiki.

Sanarwar ta ce ta ajiye aikin nata ne saboda tursasawar da ake wa masu zanga zangar neman kafa demokradiyya a Syria.

Sai dai kuma wata sanarwa da gidan talabijin na kasar Syria ya fitar daga bisani, ta musanta cewa jakadiyar ta yi murabus.

Muryar wata mata da aka sa ta ce zata kai karar kafar yada labaran Faransa da ta bada wannan sanarwa.

Tun farko an ce jama'a na ta ficewa daga garin Jisr al-Shugur dake arewacin kasar ta Syria, bisa fargabar harin da sojoji ka iya kaiwa.