Amurka ta bukaci Shugaba Saleh ya sauka

clinton Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hilary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce mika mulki ba tare da bata lokaci ba shine mafi a'ala ga al'ummar kasar Yemen.

Amurka da Saudi Arabiya suna matsin lamba na kokarin ganin an sauya mulki a Yemen a dai dai lokacin da Shugaba Ali Abdallah Saleh baya cikin kasar.

Amurka ta yi kira da a gudanarda sauyin gwamnati cikin ruwan sanyi a Yemen.

Shugaban kasar Ali Abdullah Saleh dake Saudi Arabiya ya soma murmurewa bayan tiyatar da aka yi masa sakamakon raunukanda ya samu lokacinda aka kaiwa fadarsa hari a makon daya gabata.

Saudiyya dai ta yi kira ga dukkan bangarorin da su amince da yarjejeniyar mika mulki a Yemen.

Mrs Clinton bata bayyana ko ya kamata a bar Shugaba Saleh ya koma gida ba ko kuma a'a', amma idan har ya cigaba da zama a saudi Arabia dole ne a bukaci shi ya sanya hannu a yarjejeniyar da majalisar hadin kan kasashen larabawa ta shirya don fara sauya akalar mulki.

A baya dai sau uku yana kin sanya hannu akan yarjejeniyar da Amurka ta shirya.

Can kuma a Riyadh mahukuntan Saudi Arabia suna matsawa shugaban Yemen din ya amince ya mika mulki a yayinda ita kuma Amurka ke can birnin Sana'a tana ganawa da magoya bayanshi.