Yau ne EFCC zata gabatarda Bankole gaban Kuliya

bankole Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon kakakin majalisar Wakilai Dimeji Bankole

A Najeriya a yau Laraba ne za a fara sauraron karar da Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC ta shigar a wata kotun tarayya da ke Abuja akan tsohon Kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole.

EFCC na zargin tsohon Kakakin Majalisar Dokokin kasar, Mr Oladimeji Sabur Bankole da wasu 'yan majaliasr da aikata wasu laifuka goma sha shida da suka hada da kashe kudin majalisa sama da naira miliyon dubu goma sha daya ba bisa ka`ida ba.

Kazalika Hukumar na zarginsu da kara farashin wasu motocin pijo samfurin 407 fiye da kima wadanda majalisar ta saya lokacin da yake shugabantar majalisar.

A ranar Talata ne dai EFCC ta shigar da karar bayan ta cafke tsohon kakakin a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa dake gundumar Asokoro a Abuja.