An kalubalanci hukumar EFCC a Najeriya

Tambarin Hukumar EFCC
Image caption Tambarin Hukumar EFCC

A Najeriya, yayin da Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon-kasa, wato EFCC, ke alfahari da kamen da take yi na wadansu wadanda ake ganin manya ne a siyasar kasar, Kungiyar Lauyoyi ta kasar ta ce kamata ya yi hukumar ta dage wajen ganin ta yi nasarar samun wadanda take gurfanarwa a kotu da laifi.

Hukumar dai na ikirarin cewa daga kafuwarta zuwa yanzu ta samu nasara a kan sama da mutum dari shida a shari'ar da ta yi da su a kotu, haka nan kuma tana kan tafka shari'a da sama da mutane dubu.

Ta kuma ce ta kwato kudaden da suka kai naira miliyan dubu dari tara da saba’in da biyar daga madamfara daban-daban da kuma wadansu wadanda ta kira “barayin biro ko na siyasa”.

Amma duk da haka wadansu na ganin cewa hukumar ba ta kai a yaba mata ba sakamakon zargin da suke yi cewa ta zama ’yar koren mahukuntan kasar wajen yi wa wadanda ba sa jituwa da mahukuntan bi-ta-da-kulli.

Sai dai a cewar Dakta Abubakar Othman, wani jami’in hukumar, “Tun da mu mun kware ne wajen kamawa, [wannan] ya nuna cewa a aikinmu na masu bincike [idan muka] gane akwai laifi ko kuma aka kawo mana [korafi] muka je muka bincika muka tabbatar akwai laifi, sai mu dauka mu kai kotu—ba za mu zama mu ne masu kamawa [kuma] mu ne masu yanke hukunci ba.

“Idan muka je kotu, sauran [aiki] na wajen kotu”.