An karrama wadansu likitocin Iran su biyu

Dakta Kamiar Alae
Image caption Daya daga cikin likitocin da aka karrama, Dakta Kamiar Alae

An karrama wadansu likitoci 'yan kasar Iran su biyu wadanda aka daure su a gidan yari shekaru uku da suka gabata, bisa zargin shirya makarkashiyar kifar da gwamnatin kasar.

An dai baiwa mutanen biyu kyautar yabo ta duniya a bangaren kiwon lafiya, saboda yunkurinsu na bayar da kulawa ga masu dauke da kwayoyin cutar da ke karya garkuwar jiki, wato HIV.

Daya daga cikin mutanen, Kamiar Alaei, wanda aka sako shi a farkon shekarar nan, ya amshi kyautar yabon a birnin Washington, inda ya bayyana irin kaunar da yake yiwa aikinsa da kuma cewa zai yi kokarin bunkasa bangaren lafiyar al'umma a duk iya tsawon shekarun da zai yi a duniya.

Dan uwansa kuwa, Dakta Arash Alaei, yana cikin shekara ta uku a cikin shekaru shidan da aka yanke masa a gidan yarin Tehran.

Likitocin biyu dai sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin an sanya batun kariya daga kamuwa da kwayoyin cutar HIV da kuma cutar AIDS ko SIDA a cikin ajandar tsarin lafiya a Iran.