Za a kafa hukumar bincike a Ivory Coast

Shugaba Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast

Hukumomi a kasar Ivory Coast sun bayyana cewa suna shirin kafa wata hukuma domin bincikar laifuffukan da aka aikata a kasar lokacin da tashin hankali ya barke sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamban bara.

Da ma dai shugaban kasar ta Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya yi alkawarin cewa ba za a saurarawa wadanda aka samu da hannu a keta doka ba, ciki kuwa har da nasa dakarun.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil-Adama sun ce duka bangarorin biyu sun aikata laifuffukan yaki da kuma laifuffukan cin zarafin bil-Adama a lokacin rikicin.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma kara da cewa har yanzu akwai miliyoyin al'umma da suka rasa muhallinsu a kasar ta Ivory Coast.