Jonathan ya nuna bukatar tattaunawa da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana goyon bayansa da a tattauna da kungiyar nan da ake zargi da kai hare-hare da makamai a yankunan arewacin Najeriya wadda aka fi sani da Boko Haram.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a wajen wani taro kan cutar HIV da ke gudana a birnin Washington na Amurka.

Magoya bayan kungiyar ta Boko Haram sun ce suna son a kaddamar da tsarin shari'ar Musulunci a kasar.

A baya ma dai 'yan kungiyar sun yi watsi da tayin da sabon gwamnan jihar Borno ya yi musu na tattaunawa domin kawo karshen hare-haren da suke kaiwa.

Hare-haren da magoya bayan kungiyar ke kaiwa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da suka hada da malaman addini, sarakunan gargajiya, da ma jami'an tsaro.

Kashe 'yan kasa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya shaida wa manema labarai cewa, babu gwamnatin da za ta so ta kashe 'yan kasar ta, ko da kuwa sun dauki makamai don yakar ta.

Jonathan ya ce 'yan Boko Haram 'yan kasa ne, kuma hanyar da ta fi dacewa shi ne a tattauna da su, a kuma tabbatar da cewa ba su ci gaba da daukar makamai don yakar gwamnati ba.

Ya ce gwamnatinsu ta yi nasara wajen tattaunawa da masu dauke da makamai a yankin Naija Delta, a don haka abu ne mai yiwuwa a shawo kan 'yan Boko Haram din ta hanyar tattaunawa.

A yanzu dai hare-haren bama-bamai da ake kaiwa a wasu yankunan arewacin kasar sun maye gurbin tashe-tashen hankulan da aka rika fama da su a baya a yankin Naija Deltan kasar .

Siyasa da addini

Shugaba, Jonathan ya kuma kara da cewa, hare-haren da aka kai a ranar da aka rantsar da shi, ba su da nasaba da zabe ko rantsar da shi, kuma ba su da nasaba da kasancewarsa mabiyin addinin kirista.

Jonathan ya ce kungiyar Boko Haram, kungiya ce ta musulunci da ke kai hare-hare kan kowa, musamman Musulmin da suka amince da tsarin rayuwa irin ta kasashen yammacin duniya.

Jawabin nasa na zuwa ne kwana daya bayan wasu hare-haren bama-bamai uku da aka kai a garin Maiduguri sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar ta Jama'atu Ahlulul Sunna lidda'awti wal jihad da aka fi sani da Boko Haram ne suka kai.

Sai dai shugaba Jonathan ya kara da cewa, idan tayin tattaunawa da 'yan kungiyar ta Boko Haram ya ci tura, to gwamnati za ta dauki wasu matakan na daban domin shawo kan lamarin, sai dai bai yi karin bayani kan ko wadanne irin matakai ne ba.